ABNA24 : Masu Zanga-zangar sun rika bayar da taken kin jinin ‘yan sahayoniya da kuma nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Palasdinu da kare hakkokin Palasdinawa.
A gefe daya shafukan sada zumunta na al’ummar kasar ta Bahrain, sun cika da taken yin tir da matakin na gwamnatin kasarsu na kulla hulda da ‘yan sahayoiya.
Har ila yau, wani daga cikin taken da aka rika bayarwa ya kunshi cewa; Babu yadda za a yi sulhu da ‘yan ta’adda.
Wani sashe na taken da masu Zanga-zangar su ka rika bayarwa ya kunshi cewa; Gwamnati ce ya kulla da ‘yan sahayoniya amma ba al’ummar Bahrain ba.
342/